Sojoji Sun Ceto Mutane 15 da aka sace a Zamfara

Zamafa na daga cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da bala’in ‘yan bindiga

Sojoji Sun Ceto Mutane 15 da aka sace a Zamfara

Sojoji

Dakarun soji sun hallaka wani dan bindiga kuma sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Laftanar Sulaiman Omale ya fitar a Gusau ranar Talata.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Laftanar Sulaiman na cewa, “Mun samu kiran gaggawa cewa ’yan bindiga sun kai hari yankin Tsohuwar Tasha da ke Karamar Hukumar Kauran Namoda a Jihar Zamfara, shi ne dakarunmu suka kai dauki.

“A ranar 5 ga Maris, 2024, sojojin sun yi mummunar artabu da ’yan bindigar, wanda hakan ya tilastawa ’yan bindigar tserewa, wasu suka fada ruwa.

“A yayin da suke bin sawun ’yan bindigar da suka gudu, sojoji sun kashe daya daga cikin maharan, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga.”

A cewarsa, wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da mata takwas da maza bakwai.

“A yanzu dai zan iya cewa zaman lafiya ya samu a yankin, kuma mutane sun samu kwarin gwiwa, ganin yadda dakarunmu ke ci gaba da sintiri”.

Babban kwamandan sojin runduna ta 8, da ke Sakkwato, Manjo-Janar Godwin Mutkut, ya yaba da kwazo da kuma jajircewar sojojin.

Mutkut ya yi kira ga sojoji su dage, su ninka kokarin da suke yi har sai an samu cikakken zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma da ma duka fadin Najeriya.

Jihar Zamafa dai daya ce daga jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da bala’in ’yan bindiga.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna