Sojoji sun ceto mutane 53, sun fatattaki mayakan ISWAP a Borno

Nan da nan aka tura rundunar sojoji mai ƙarfi daga Dutsen Kura, wadda ta bi sawun ’yan ta’addan zuwa yankin Mangari–Dora, ta yi musu luguden wuta, wanda ya tilasta musu tserewa

Sojoji sun ceto mutane 53, sun fatattaki mayakan ISWAP a Borno

Wasu daga cikin mutanen da sojojin suka kubutar bayan fatattakar mayakan ISWAP a hanyar

Dakarun sojin Najeriya sun sun ceto fararen hula 53 tare da kwato motoci takwas bayan sun rushe wani shingen hanya da ’yan ta’addan ISWAP suka kafa a kan babbar hanyar Buratai zuwa Kamuya, a Karamar Hukumar Biu, Jihar Borno.

Sanarwar da mukaddashin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Operation HADIN KAI,, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ta bayyana cewa, sojojin Bataliyar ta Musamman ta 135 ƙarƙashin Sashe na 2 ne suka fara aikin bayan kyamarorin sa ido sun gano ’yan ta’addan da ake zargi da toshe hanyar.

A cewarsa, nan da nan aka tura rundunar sojoji mai ƙarfi daga Dutsen Kura, wadda ta bi sawun ’yan ta’addan zuwa yankin Mangari–Dora, ta yi musu luguden wuta, wanda ya tilasta musu tserewa su bar shingen da suka kafa.

Sojojin sun ceto fararen hula 53, tare da kwato motoci takwas da ’yan ta’addan suka sace. Daga bisani, sojojin suka share hanyar da aka mamaye, sannan suka kwashe fararen hular da aka ceto zuwa garin Buratai, tare da motoci da sauran kadarorin da aka kwato, inda ake ci gaba da bincike da tantance lafiyarsu.

Wasu daga cikin matafiyan da sojoji suka kubutar a yayin aikin

 

Kyaftin Goni ya yaba da ƙwarewar sojojin da kuma saurin mayar da martani, yana mai bayyana aikin a matsayin babbar nasara a ci gaba da fatattakar ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas.

Motocin matafiyan da mayakan ISWAP suka tare a hanyar kafin sojoji su kai dauki

Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su kasance cikin shiri da lura, tare da ci gaba da samar da bayanai kan duk wani abin da ake zargi ga hukumomin tsaro.

Sojojin sun ƙara da cewa yanayin tsaro a yankin ya ci gaba da samun kwanciyar hankali, a yayin da dakarun ke aiki tuƙuru don hana ’yan ta’adda sake taruwa da kuma kare al’ummomi a faɗin yankin.