Sojoji sun ceto mutum 13 da ’yan bindiga suka sace a Zamfara
Dakarun sun jadadda ƙudirin ci gaba da yaƙi da laifuka a yankin.
Dakarun Sojin Rundunar Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutum 13 da aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare daban-daban da suka auku a Ƙananan Hukumomin Anka da Kaura Namoda na Jihar Zamfara.
Rundunar ta ce an gudanar da waɗannan ayyuka ne a ranar Laraba bayan samun bayanan sirri kan shirye-shiryen wasu ’yan ta’adda na kai hare-hare a yankunan.
A Ƙaramar Hukumar Anka, sojojin sun bi sahun wasu ’yan ta’adda da ke kan babura bayan sun nufi ƙauyen Tungan Kudaduku.
Bayan musayar wuta, ’yan ta’addan sun tsere cikin daji, inda suka bar wani sansani da sojoji suka gano tare da ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.
A wani samame na daban a Ungwan Rogo da ke Kaura Namoda, sojojin sun yi artabu da ’yan ta’addan da ke ƙoƙarin tserewa, lamarin da ya sa suka bar mutane takwas da suka yi garkuwa da su.
Sojojin sun kuma ƙwato motoci biyu da ake zargin maharan sun bari yayin tserewa.
Rundunar ta ce ta miƙa dukkanin mutane 13 da ceto ga hukumomin da suka dace domin ba su kulawa.
Ta ƙara da cewa sojoji za su ci gaba da gudanar da ayyuka domin daƙile hare-haren ’yan ta’adda da tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.