Sojoji sun ceto mutum 22 da aka yi garkuwa da su a Sakkwato
Rundunar soji ta Operation Fansan Yamma ta ceto mutane 22 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kananan Hukumomin Sabon Birni da Isa na Jihar Sakkwato.
Wasu daga cikin mutanen da sojoji suka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Sakkwato
Rundunar soji ta Operation Fansan Yamma ta ceto mutane 22 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kananan Hukumomin Sabon Birni da Isa na Jihar Sakkwato.
Kakakin Rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya ce an gudanar da ayyukan ceton ne bayan samun sahihin bayanan sirri da kuma kiran gaggawa daga al’umman da abin ya shafa.
Ya ce, da farko a ranar 18 ga Yuni, 2026, sojoji sun kai dauki bayan samun rahoton cewa ’yan ta’adda sun tare hanyar Sabon Birni-Shinkafi a kauyen Kura Mota, inda suka kai wa wasu motoci biyu hari, inda suka kashe fasinja daya suka sace wasu da dama.
Danja ya ce cikin gaggawa sojoji suka isa wurin tare da bin sawu lamarin day a tilasta wa ’yan ta’addan tserewa su bar mutane su 17, da suka yi garkuwa da su, inda daga bisani aka mika su ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakan da suka wajaba.
- Bom din ’yan ta’adda ya kashe sojoji a Sakkwato
- Matashi ya rasu a gidan budurwarsa a Kano
- Katsina: Sojoji sun ceto wanda aka sace, sun lalata sansanin ’yan bindiga
A wani lamari makamancin haka, Danja ya ce sojoji sun kai dauki a kauyen Chohi a ranar, inda ’yan ta’addan suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da manoma a gonakinsu.
Ya ce sojoji sun garzaya wurin cikin gaggawa, suka bi sawun ’yan ta’addan, wanda hakan ya kai ga ceto manoma biyar da aka yi garkuwa da su, aka mika su ga iyalansu.
Bayan kammala aikin ceto, ya ce sojoji sun gudanar da sintirin ƙarfafa gwiwa a cikin al’umman da ke kewaye, ciki har da kauyukan Gidan Rana da Gidan Sale, domin kwantar da hankalin jama’a, mamaye yankin da kuma hana ‘yan ta’adda samun damar yin aiki.
Ya ce ayyukan sun nuna jajircewar rundunar Operation Fansan Yamma wajen kare rayuka da dukiyoyi, tsare al’umman da ke cikin haɗari da kuma samar da yanayi mai tsaro domin ’yan ƙasa su gudanar da ayyukansu na halal ba tare da tsoro ba.