Sojoji sun ceto mutum 47 daga hannun ’yan ta’adda a Borno

Waɗanda aka ceto sun kuɓuta ne a sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa maɓoyar ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.

Sojoji sun ceto mutum 47 daga hannun ’yan ta’adda a Borno

Sojojin rundunar Operation Haɗin Kai sun ceto mutum 47, galibi mata da yara, daga hannun ’yan ta’addan ISWAP a yankin Kangarwa da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Wata sanarwa da muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Operation Haɗin Kai ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Litinin, ta ce an gudanar da aikin ceton ne a ranar 20 ga watan Yunin da muke ciki.

Goni ya ce waɗanda aka ceto sun shaƙi iskar ’yanci ne a sakamakon ci gaba da hare-haren da sojoji ke kai wa maɓoyar ’yan ta’addan ISWAP a yankin Tafkin Chadi.

“Rundunar Operation Haɗin Kai ta samu wani gagarumin nasara ta ceto mutum 47, galibi mata da yara, waɗanda ’yan ta’addan ISWAP suka tsare a Kangarwa da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno a ranar 20 ga Yuni, 2026,” in ji sanarwar.

Ya bayyana cewa an samu nasarar aikin ne sakamakon matsin lamba da hare-haren ƙasa da na sama da sojoji suka tsananta kai wa sansanonin ’yan ta’addan.

“Ana ci gaba da kai hare-haren ƙasa da na sama kan sansanonin ISWAP a yankin Tafkin Chadi, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan barin maboyarsu cikin ruɗani.

“Hakan ya bai wa waɗanda aka tsare damar tserewa daga zaman bauta da suka shafe lokaci mai tsawo suna ciki,” in ji shi.

A cewarsa, waɗanda aka ceto suna samun kulawar likitoci da sauran tallafin jin ƙai a wani wuri mai tsaro.

“A halin yanzu ƙwararrun likitoci suna duba lafiyarsu, yayin da ake ba su tallafin da suka dace tare da haɗin gwiwar hukumomin da abin ya shafa domin sauƙaƙa sake shigar da su cikin al’umma,” in ji sanarwar.

Goni ya ce nasarar ceton mutanen na nuna jajircewar sojoji wajen kare fararen hula da kuma raunana hanyoyin sadarwa da ayyukan ’yan ta’addan a yankin Arewa maso Gabas.

“Wannan nasara ta sake nuna ƙudirin rundunar wajen rage ƙarfin ’yan ta’adda da kuma ma kuɓutar da fararen hula da aka kama ba tare da son ransu ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da kai hare-hare domin wargaza sauran sansanonin ISWAP da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

“Kwamandan rundunar ya sake jaddada aniyar ci gaba da kai farmaki, wargaza sauran hanyoyin sadarwar ISWAP da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Arewa maso Gabas,” in ji sanarwar.

Jihar Borno dai ta shafe sama da shekara goma tana fama da matsalar ta’addanci, inda dubban mutane suka rasa matsugunansu, wasu kuma aka kashe ko aka sace sakamakon hare-haren Boko Haram da ISWAP.

A cikin ’yan watannin nan, sojoji sun ƙara zafafa hare-hare a yankunan Tafkin Chadi da Dajin Sambisa a wani yunƙuri na raunana ƙungiyoyin ta’addanci da kuma tabbatar da tsaron al’ummomin da rikicin ya shafa.