Sojoji sun ceto mutum 7 daga hannun ’yan bindiga a Filato
Dakarun sun yi artabu da ‘yan bindigar kafin daga bisani suka ceto waɗanda aka sace.

Jami’an tsaro a Jihar Filato, sun ceto mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace.
An gano mutanen a yankin Ganawuri, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom, bayan da sojojin Operation SAFE HAVEN (OPSH) suka kai farmaki maɓoyar ’yan bindigar.
- Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai
- Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai
An gudanar da aikin ceton ne a matsayin wani ɓangare na Operation LAFIYAN JAMA’A, wanda ke da nufin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya bayyana cewa sojojin sun samu bayanan sirri cewa an ɓoye wasu mutane da aka sace a kusa da hanyar Jos zuwa Ganawuri.
“Yayin farmakin, sojojinmu sun yi arangama da ‘yan bindigar, amma sun tsere bayan sun fuskanci ruwan wuta.
“Daga nan, sojojin suka bi sahu suka kuma ceto mutum bakwai da maharan suka sace,” in ji Manjo Zhakom.
An bayyana sunan mutanen da aka ceto, waɗanda dukkaninsu ‘yan asalin Jihar Bauchi ne: Sale Umar, Muhammadu Inusa, Abdullahi Abdulrasaq, Abdulsalam Muhammad, Muhammad Hamisu, Ibrahim Maradu, da Saidu Sani.
Sojojin sun kuma gano wata jaka mai ɗauke da bargo da kaya da ‘yan bindigar suka bari.
Sun yi wa mutanen da suka ceto tambayoyi don taimakawa musu da bayanan da za su sa a kama ‘yan bindigar da suka tsere.