Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
Gwamnatin ta jaddada aniyarta na ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga a jihar.

Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 84 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa sojojin runduna ta 17 tare da tallafin jiragen yaƙi sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’adda da ke yankin Sanusi Dutsin-Ma da tsaunukan Pauwa.
- ’Yan bindiga sun sace shugaban kasuwar kayan miya ta Akinyele a Oyo
- Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira
Ya ce a yayin farmakin dakarun sun kashe wasu daga cikin ’yan bindiga sannan suka kuɓutar da waɗanda aka sace.
Daga cikin mutanen da aka ceto, akwai maza bakwai, mata 23, da yara 54.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta yaba wa sojojin bisa ƙoƙarinsu, kuma tuni aka samar da abinci da kulawa ga mutanen da aka kuɓutar, kafin a mayar da su ga iyalansu.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Katsina ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba, domin tana da niyyar ci gaba da yaƙi da su har sai an daƙile matsalar garkuwa da mutane a jihar.