Sojoji sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa a Zamfara
An gudanar da aikin ceton ne a ranar 22 ga watan Yuni yayin wani sintiri na fatattakar ɓata-gari a yankin Bagega da ke ƙaramar Hukumar Anka a Jihar Zamfara.
Rundunar Sojojin Sashe na 2 na Haɗin Gwiwar Jami’an Tsaro na Shiyyar Arewa maso Yamma, ƙarƙashin rundunar Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su.
Sojin kuma sun daƙile wani hari na ta’addanci yayin wasu farmaki daban-daban da suka kai a jihohin Zamfara da Sakkwato.
- An umarci bankuna su rufe asusun masu alaƙa da ta’addanci
- Matsalolin tsaro na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi a Sakkwato — Gwamna Aliyu
Wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Operation Fansan Yamma, Leftanal Kanal Aliyu Danja ya fitar ta bayyana cewa, an gudanar da waɗannan ayyukan tsaro ne a matsayin ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ta’addanci da fashi da makami a faɗin shiyyar Arewa maso Yamma.
Leftanal Kanal Danja ya kuma bayyana cewa, wannan samame ya kai ga ƙwato wani babban makami na musamman, alburusai da babura da sauran kayayyakin aiki na ’yan ta’addan.
Jami’in yaɗa labaran ya ƙara da cewa, an gudanar da aikin ceton ne a ranar 22 ga watan Yuni yayin wani sintiri na fatattakar ɓata-gari a yankin Bagega da ke ƙaramar Hukumar Anka a Jihar Zamfara.
A cewarsa, masu garkuwan sun tsere sun bar mutanen da suke tsare da su ne sakamakon matsin lamba da zaratan sojojin da ke aiki a yankin suka yi ta yi musu.
An gano waɗanda aka ceton kamar haka: Zainab Muhammadu mai shekara 28 daga ƙauyen Gara Zaima a ƙaramar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara; da Hafsat Ibrahim ’yar shekara 20 da kuma Halira Usman ’yar shekara 17, dukkansu daga ƙauyen Mashiga/Taka Lafiya da ke ƙaramar Hukumar Zuru a Jihar Kebbi.
Leftanal Kanal Aliyu Danja ya kuma bayyana cewa, waɗanda aka yi garkuwan da su sun kwashe kimanin watanni uku a tsare a hannun masu garkuwan kafin su samu ’yancinsu, inda daga bisani aka kwashe su domin ba su kulawar lafiya da sauran abubuwan da suka dace.
