Sojoji sun ceto ragowar ɗaliban Kogi 8 da aka sace 

Ɗaliban sun shafe sama da wata biyu a hannun ‘yan bindiga.

Sojoji sun ceto ragowar ɗaliban Kogi 8 da aka sace 

Dakarun sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, sun ceto sauran ɗaliban Jami’ar Confluence University of Science and Technology (CUSTECH), da aka sace a Jihar Kogi.

Aminiya ta ruwaito aka yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar 32 a farkon watan Mayu lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar.

Sai dai maharan sun kashe ɗalibai biyu daga cikin waɗanda suka sace, yayin da jami’an tsaro suka yu nasarar kubutar da 30 daga hannun maharan.

Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a shafinta na X (Twitter) a ranar Lahadi, ta ce sojojin a wani samame da suka kai, sun kuɓutar da sauran ɗaliban da suka rage a wani daji da ke kusa da ƙauyen Oro Ago a Jihar Kwara.

Sanarwar, ta ce sojojin a yayin samamen, sun gano inda aka ɓoye ɗaliban.

A cewar sanarwar, an gudanar da binciken ne a yankin Gbugu, Pategi, da Oro Ago, ciki har da yankunan Babasango da Babanla.

“Saboda haka, sojoji sun gano inda ‘yan ta’addan da suka ɓoye ɗaliban, yayin da sojoji suka yi musu ruwan wuta tare da ceto ɗaliban.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ɗaliban da aka ceto na cikin ƙoshin lafiya sannan an miƙa su ga hukumomin gwamnatin Jihar Kogi domin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace.”

Rundunar sojin Najeriya ta buƙaci jama’a da su zama masu sanya ido tare sa kai rahoton ayyukan ɓata-gari ga hukumomin tsaro.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania