Sojoji sun ceto ’yan mata biyu da suka tsere daga hannun ’yan ta’adda a Borno

’Yan matan da aka ceto sun haɗa da Bintu Adamu, mai shekara 15, da Sadiya Jummai, mai shekara 11.

Sojoji sun ceto ’yan mata biyu da suka tsere daga hannun ’yan ta’adda a Borno

Dakarun Bataliya ta 82 da ke ƙarƙashin rundunar Operation HADIN KAI sun ceto wasu ’yan mata biyu da suka tsere daga sansanin ’yan ta’adda a tsaunukan Mandara da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Aminiya cewa an gano ’yan matan ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar ranar 2 ga Yuli, yayin da sojojin da aka tura Ngoshe ke gudanar da sintiri na yau da kullum a yankin mai tsaunuka.

Majiyoyin sun bayyana cewa, jami’an sintirin sun hango ’yan matan biyu a kusa da gadar Armuda, inda suka tunkare su cikin taka-tsantsan kafin suka tabbatar cewa fararen hula ne da ke cikin mawuyacin hali.

’Yan matan da aka ceto sun haɗa da Bintu Adamu, mai shekara 15, da Sadiya Jummai, mai shekara 11.

Sojojin sun ci gaba da gudanar da sintiri a yankin da ke kewaye bayan ceto ’yan matan domin tabbatar da cewa babu wata barazana kafin su koma sansaninsu lafiya.

Binciken farko ya nuna cewa ’yan ta’adda ne suka sace ’yan matan a garin Ngoshe, inda suka tsare su a wani sansani da ke yankin China a tsaunukan Mandara.

Rahotanni sun ce ’yan matan sun yi amfani da wata dama suka sulale daga hannun maharan, kafin daga bisani su haɗu da sojojin da ke sintiri a yankin.

Nan take dakarun suka ba su agajin gaggawa, sannan suka miƙa su ga shugaban al’ummar Ngoshe, Malam Bulama Kunda, kuma tuni an mayar da su wurin iyalansu.

Rundunar ta ce wannan nasara na nuna ci gaba da ƙoƙarin da dakarun Operation HADIN KAI ke yi wajen ceto waɗanda aka sace, rusa maɓoyar ’yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin da rikici ya shafa a yankin Arewa maso Gabas.