Sojoji sun ci gaba da kai wa jaridun Daily Trust hari
Sojoji sun ci gaba da kai hari kan jaridun a sassan kasar nan, inda a ranar Talatar da ta gabata suka hana jaridar Daily Trust shiga Sakkwato na awa shida.Sojojin sun fara kai farmaki ne kan jaridun da suka hada da Daily Trust da Aminiya da jaridun Leadership da The Nation a ranar Juma’ar da […]
Sojoji sun ci gaba da kai hari kan jaridun a sassan kasar nan, inda a ranar Talatar da ta gabata suka hana jaridar Daily Trust shiga Sakkwato na awa shida.
Sojojin sun fara kai farmaki ne kan jaridun da suka hada da Daily Trust da Aminiya da jaridun Leadership da The Nation a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka ce suna yin haka ne saboda dalili na tsaro.
A ranar Lahadi suka tsagaita kai harin, amma suka koma a ranar Talata, inda da misalin karfe shida na safe suka kame jaridun Daily Trust a garin Tsafe a kan hanyar kai su Sakkwato.
An tsare motar daukar jaridun da direbana na wa shida kafin a bar shi ya wuce lamarin da ya sa ba ta isa ga dimbin makarantarta ba.
A ranar Asabar da ta gabata mahukunta Daily Trust sun fitar da wata sanarwa suna la’antar matakin da sojojin suke dauka a kan jaridun kamfanin.
Kamfanin ya koka kan yadda aka kama masu rarraba jaridu da direbobi tare da tsare biyu daga cikinsu Ibrahim Umar da Iliya Mohammed na fiye da awa 24. Kuma a Abuja an girka motocin soja hudu a wurin da aka fi rarraba jaridun kamfanin da ke Area One.
“Sojoji dauke da miyagun makamai sun nace sai sun aiwatar da ‘umarni daga sama’ inda suka rika wargaza dubban kwafe na jaridunn Weekly Trust da sunan bincikar ‘abubuwa masu hadari da ake zargi,’ inji sanarwar Daily Trust.
Kuma a cewar sanarwar duk da ba su gano wani abu ba, sun hana ma’aikatan kamfanin da masu sayar da jaridun gudanar da halattaciyar harkarsu ta neman abinci.
A ranar Asabar an hana kai jaridun zuwa jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Sakkwato da Jigawa da Kebbi da Katsina da Zamfara daga madaba’ar kamfanin da ke Kano.
Sannan kwafen jaridun da ake sayarwa a jihohin Arewa maso Gabas ma an hana su shiga kasuwa a kokarin hana makaranta samun jaridun a jihohin Adamawa da Gombe da Bauchi da Taraba da Yobe.
Idan za a iya tunawa wanim labari da jaridar Daily Trust ta buga a makon jiya wanda ya fallasa yadda manyan jami’an soja da suka yi ritaya suka rarraba wa kansu da iyalansu wani fili da aka ware don gina barikin soja a yankin Asokoro da ke Abuja, kuma ana jin wannan labarin ne ya fusata sojojin daukar wannan mataki.