Sojoji sun dakile harin bam uku a Gamboru
Sojojin Najeriya sun yi nasara dakile tashin bama-bamai uku da wasu ’yan kunar bakin wake ke dauke da su da nufin halaka al’umma a karamar Hukumar Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Mataimakin Daraktan yada labarai na shirin ‘Operation Lafiya Dole’ Kanal Onyema Nwachukwu ya bayyana haka ne ga manema labarai, a a wata sanarwa […]

Sojojin Najeriya sun yi nasara dakile tashin bama-bamai uku da wasu ’yan kunar bakin wake ke dauke da su da nufin halaka al’umma a karamar Hukumar Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.
Mataimakin Daraktan yada labarai na shirin ‘Operation Lafiya Dole’ Kanal Onyema Nwachukwu ya bayyana haka ne ga manema labarai, a a wata sanarwa da ya raba masu.
Kamar yadda ya ce, ’yan kunar bakin waken biyu suna sanya da rigunan bama-bamai, a inda suka shiga garin Gamboru da misalin karfe shida da minti arba’in da biyar na safiyar Talatar da ta gabata, wanda Allah Ya sa wani dan banga da ke bakin aiki ya hango su a Unguwar Yobe bayan sun shigo.
Ya ci gaba da cewa, sojoji da ’yan banga suka yi maza suka dakatar da su, suka bukaci su cire rigunan bam din da suke sanye da su amma suka ki. “Ganin haka ya sanya sojoji masu aikin dakile bam suka yi iya kokarinsu wajen kwance bama-baman, suka hana su tashi,” inji shi.
Kanal Onyema ya ce, bayan sun kammala da wadannan ’yan kunar bakin waken sai suka sake gano mace daya tare da wannan rigar bama-baman, a wannan wajen kuma suka dakatar da ita.
Ganin hakan ya sa ta tsorata ta ce da su akwai wadansu ’yan kunar bakin wake biyu, wadanda suka shigo masu kuma sun yi niyyar tada bama-baman da misalin karfe 3:30 na safe a garin Gamboru.
Yarinyar ta fallasa inda sauran rigunan bama-baman suke ajiye da kuma wadannan ’yan kunar bakin wake da suka yi niyyar tada bama-baman. Jin hakan ya sanya sojoji suka je wajen suka kame wadannan,suka kai su ofishinsu domin amsa tambayoyi.
Onyema ya yi kira ga jama’a da su kula sosai da irin mutanen da ke shiga wajensu idan sun bar gida kuma su kawo karar duk wanda suke zargin dan Boko Haram ne.