Sojoji sun dakile harin Boko Haram sun kashe 39

Rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da ‘yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, MNJTF, sun kashe mayakan Boko Haram 39 tare da kwato makamai masu yawa a hannun su, a yayin arangamar sojoji 20 sun samu raunuka. Kakakin rundunar sojojin Kanal Timothy Antigha, ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da yake ganawa […]

Sojoji sun dakile harin Boko Haram sun kashe 39

Rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da ‘yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, MNJTF, sun kashe mayakan Boko Haram 39 tare da kwato makamai masu yawa a hannun su, a yayin arangamar sojoji 20 sun samu raunuka.

Kakakin rundunar sojojin Kanal Timothy Antigha, ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya Laraba a Abuja.

Kanal Timothy, ya ce an kashe maharani ne a yankin Cross Kauwa jihar Borno ranar Talata yayin da wadanda aka raunata yanzu haka suke asibiti suna jinya.