Sojoji Sun Dakile Harin ISWAP A Mafa

Mayakan ISWAP sun mamaye garin a cikin manyan motoci suka rika kai hari da manyan bindigogi kan sojojin

Sojoji Sun Dakile Harin ISWAP A Mafa

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun yi dakile wani hari da aka kai da tsakar dare a Karamar Hukumar Mafa da ke Jihar Borno.

’Yan ta’adda da dama da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP sun mamaye garin a cikin manyan motoci da babura, inda suka rika kai hari da manyan bindigogi kan sojojin.

Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro da yaki da ta’addanci a Yankin Tafkin Chadi, cewa sojojin sun dakile harin ne baya artabu da ’yan ta’addan.

Majiyar ta ce “Sun yi yunkurin kai mana hari ta hannun Charly Papa 1, amma mun samu nasarar dakile munanan shirin nasu,  kuma mun yi wa ’yan ta’addan mumunan barna.

“Mun tilasta musu ja da baya suka gudu, sun yi watsi da mugunyar manufar tasu ba a samu asarar rayuka a bangaren sojojin ba,” in ji majiyar.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya