Sojoji sun damke ’yan Boko Haram a Dutse
Rundunar tsaro ta JTF daga Damaturu ta kai samame garin Dutse da ke Jihar jigawa inda ta damke wani da ake zargin yana da alaka da kungiyar Boko Haram mai suna Mu’awiyya Gurduba da kuma kanensa mai suna Yunusa Gurduba.Sojojin dauke da manyan bindigogi sun kai samame kan titin babbar hanya da ke Dutse lamarin […]
Rundunar tsaro ta JTF daga Damaturu ta kai samame garin Dutse da ke Jihar jigawa inda ta damke wani da ake zargin yana da alaka da kungiyar Boko Haram mai suna Mu’awiyya Gurduba da kuma kanensa mai suna Yunusa Gurduba.
Sojojin dauke da manyan bindigogi sun kai samame kan titin babbar hanya da ke Dutse lamarin da ya sa mutanen da ke kusa da inda Mu’awiyya yake sayar da kayan gwanjo suka shiga cikin rudani.
Wani wanda ya gane wa idonsa lamarin kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sojojin na isa wurin suka yi harbin iska domin sannan suka farfasa tayoyin babura da motocin da ke wurin a kokarinsu na kama wanda suke zargin.
Binciken da wakilimmu ya yi ya gano cewa sojojin sun kai irin wannan samame Sabuwar Kasuwa da ke Dutse inda suka damke wani mai suna Sunusi kanen Mu’awiyya a inda yake sayar da gwanjo da wani mai suna Yahuza inda daga baya sojojin suka saki Yahuza saboda ba ya da alaka da kungiyar.
Wata majiya ta shaida wa wakilimmu cewa sojoji sun yi gaba da wadanda ake zargin kuma ana zargin Mu’awiyya yana daya daga cikin wadanda Rundunar JTF suke nema ruwa a jallo saboda kasancewarsa babba a cikin kungiyar ta Boko Haram
Aminiya ta gano cewa kafin damke Sunusi yana da shaguna a layin Masallacin Juma’a na kusa da Masallacin Izala da ke Dutse kuma yana daya daga cikin manyan dillalan a harkar gwanjo a Dutse. Wata majiya ta ce tun dawowarsa jihar mutane suke zargin watakila yana da alaka da Boko Haram ganin yadda yake facaka da kudi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ASP Abdu Jinjiri ya ce sun samu labarin sojojin sun zo jihar amma ba ya da cikakken bayani a kai, saboda ba sa nan a lokacin da abin ya faru suna ziyarar aiki a masarautar Hadeja da Kazaure.