Sojoji sun fafata da ’yan Boko Haram a Kaduna
Ranar Asabar din nan da ta wuce ne wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka bindige wani soja a lokacin wani gumurzun da suka yi a wani gida da misalin karfe 1:00 na dare a kauyen Kekebi (KKB) a karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna. Rahotanni sun ce wani hadin gwiwar […]
Ranar Asabar din nan da ta wuce ne wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka bindige wani soja a lokacin wani gumurzun da suka yi a wani gida da misalin karfe 1:00 na dare a kauyen Kekebi (KKB) a karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce wani hadin gwiwar jami’an tsaro na sojoji da ’yan sanda da kuma SSS ne suka kai hari gidan da ’yan bindigar ke zaune da niyyar kama su.
Kuma bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa kama ’yan bindigar ya ci tura sakamakon bude wa tawagar jami’an tsaron wuta da suka yi da manyan bindigogi.
Makwabtan gidan da abin ya faru sun bayyana wa Aminiya cewa an dauki sa’o’i ana musayar wuta da ’yan bindigar inda daga bisani suka harbe soja daya suka raunata daya sannan suka gudu daga gidan.
Bayan sun gudu ne sojoji suka samu nasarar shiga cikin gidan suka kama matansu da ’ya’yansu suka yi gaba da su.
Aminiya ta ga yadda gidan ya lalace sakamakon ruwan harsashi da aka yi tsakanin ’yan bindigar da jami’an tsaron.
Dagaci kauyen Malam Suleiman Mohammed ýya ce sun fara jin karar bindigogi ne da misalin karfe 1:00 na dare. “Da misalin karfe daya na dare ne sai muka ji motocin sojoji na ta shigowa har suka je suka tsaya a kusa da kofar gidan wakilina. Tun daga nan sai muka fara jin karar bindigogi hakan ya sa ba mu yi barci ba har gari ya waye. Mun samu labarin abin da ya faru kuma sojojin sun ce akwai wadanda suke nema ne, mu kuma al’ummar garin ba mu san kammanin wadannan mutane ba, sai dai mu ce Allah Ya sauwake,” inji shi.
Bayanai sun nuna cewa wadanda ake zargin ba su dade da kama a haya a gidan da abin ya faru ba.
“Gaskiya ba su wuce wata shida zuwa bakwai ba da zuwa gidan ba. Kuma ba a dade da kawo wata amarya cikin gidan ba daga Bauchi. Gaskiya mun ga firgici domin tun yakin Biyafara rabona da jin irin karar bindigogin da na ji,” inji wani makwabcin gidan da abin ya faru da ba ya son a ambaci sunansa.
kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar Soji ta daya da ke Kaduna ya ci tura, inda ya ki daukar wayar wakilinmu.