Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga a Arewa ta tsakiya
Hedikwatar tsaro ta ce dakarun sojin Opertaion Whirl Stroke da ke aikin a yankin Arewa ta tsakiya sun kara samun gagarumar nasara a aikin nasu na dakile manyan laifuka. Kakakin Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche a ranar Talata ya ce, sojoji sun yi wa ’yan bindiga ruwan wuta suka kuma tarwatsa maboyarsu a dazukan […]
Wasu sojojin Najeriya
Hedikwatar tsaro ta ce dakarun sojin Opertaion Whirl Stroke da ke aikin a yankin Arewa ta tsakiya sun kara samun gagarumar nasara a aikin nasu na dakile manyan laifuka.
Kakakin Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche a ranar Talata ya ce, sojoji sun yi wa ’yan bindiga ruwan wuta suka kuma tarwatsa maboyarsu a dazukan da ke kan iyakar jihohin Binuwai da Nasarawa.
- Sojoji sun bindige kasurgumin dan ta’addan Binuwai
- Masu garkuwa sun kashe jami’in DSS a Jihar Katsina
Bayan samun bayanan sirri, sojoji sun kai samame a maboyar yaran Terwase Gana da aka hallaka a yankin Adu na Karamar Hukumar Chanchangi na Karamar Hukumar Takum ta Jihar Taraba.
A nan ne bata-garin suka bude wa sojoji wuta, su kuma “suka mayar da martani da makaman da suka fi nasu yan daban wadanda nan take suka ranta a na kare zuwa cikin jeji.
“An kashe ’yan bindiga biyu a sansanin aka kuma kwato kananan bindigogin hannu kirar gida a wurinsu.
Rundunar ta kuma tsare wasu mutum uku da take zagi da laifi inda suka kwato wayoyin hannu 16 da layu da tabar wiwi.
“Yanzu ana bincikarsu kafin a mika su ga ’yan sanda.
“Yanzu sojoji sun mamaye yankin inda suke sintiri domin hana ‘yan bindigar samun sakat a yankin”, inji Enenche.