Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga sun ceto mutum 4 a Taraba

Maharan sun tsere bayan shan ruwan wuta daga dakarun sojin.

Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga sun ceto mutum 4 a Taraba

Dakarun Sojin Najeriya tare da hadin gwiwar ’yan sanda sun lalata maboyar ’yan bindiga tare da ceto wasu mutum hudu a Karamar Hukumar Yorro a Jihar Taraba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Olabodunde Oni, ya fitar a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa sun tarwatsa maboyar ’yan bindigar da suka addabi yankin Yorro da kewaye.

Ya ce sojojin sun yi arangama da ’yan bindiga a tsaunin Gampu da yankin Ban Yorro, inda suka yi wa ’yan ta’addan ruwan wuta.

“Har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin ceto wadanda aka sace a yankin tare da hada su da iyalansu.

“Rundunar soji ta jadadda aniyar tabbatar da tsaron lafiyar ’yan kasa da kuma tarwatsa masu aikata laifuka a jihar nan.

“An yi kira ga jama’a da su bai wa sojoji goyon baya ta hanyar bayar da sahihan bayanai don taimakawa wajen inganta tsaro.”