Sojoji sun fitar da sunayen mutum 97 da suke nema ruwa a jallo

A Arewa maso Tsakiya da Kudu maso Gabas mutum 21 ne hukumar ta sanar tana nema ruwa a jallo.

Sojoji sun fitar da sunayen mutum 97 da suke nema ruwa a jallo

Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta fitar da sunaye da hotunan mutum 97 waɗanda ta ce tana nema ruwa-a-jallo kan zarginsu da ayyukan ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da kuma barazana ga tsaron ƙasar.

Daraktan Watsa Labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja.

Mutanen da ake nema sun ƙunshi ’yan ta’adda da kwamandojinsu daga Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya da Kudu maso Gabashin Nijeriya.

Bisa sunaye da hotuna da hedikwatar tsaron ta fitar, mutum 43 daga Arewa maso Yammacin Nijeriya suke inda daga cikinsu akwai Alhaji Shingi, Malindi Yakubu, Boka, Dogo Gide, Halilu Sububu, Ado Aliero, Bello Turji, Dan Bokkolo, Labi Yadi, Nagala, Saidu Idris, Kachalla Rugga, Sani Gurgu, Dogo Nahali, Maundi, Boka,  Leko, Maman Kabiru, Kinshasa Muktar, Nasanda, San Dangote, Saidu Idris, Danda da Laibi.

A Arewa maso Gabashin Nijeriya kuwa, wanda yanki ne da Ƙungiyar Boko Haram ta addaba, akwai mutum 33 da hedikwatar ta lissafo waɗanda ta ce su ne suka addabi yankin.

Daga cikinsu akwai Abu Zaida, Modu Sulum, Baba Data, Ahmad, Sani Teacher, Ba’a Sadiq, Abdul Saad, Kaka Abi, Mohammad Khalifa, Umar Tella, Abu Mutahid, Mallam Mohammad, Mallam Tahiru Baga, Uzaiya da Ali Ngule, Abu Fatima, Baba Ngule,  Baba Data da Modu Sulum.

A Arewa Maso Tsakiya da Kudu maso Gabas mutum 21 ne hukumar ta sanar tana nema.

Daga cikin waɗanda ake nema Kudu maso Gabashin Nijeriya akwai jagoran ɗayan reshen ƙungiyar IPOB, Simon Ekpa.

Haka kuma, Chika Edoziem, Egede, Zuma, ThankGod Gentle, Flavour, Mathew, David Ndubuisi, High Chief Williams Agbor, Ebuka Nwaka da kuma Friday Ojimka.

Ana iya tuna cewa, a watan Nuwambar 2022 Hedikwatar Tsaron ta fitar da sunayen wasu ’yan ta’adda 19 da take nema ruwa a jallo tare da sanya tukwicin Naira miliyan biyar kan kowannensu.

Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba

HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja