Sojoji sun gano haramtacciyar masana’antar ƙera makamai a Filato

Ainihin mamallakin masana’antar ya gudu amma ana neman sa don gurfanar da shi a gaban shari’a.

Sojoji sun gano haramtacciyar masana’antar ƙera makamai a Filato

Rundunar Hakorin Damisa a yayin kai samame masana’antar kera makamai a Filato

Dakarun Hakorin Damisa na rundunar sojin Nijeriya sun gano wata haramtacciyar masana’antar ƙera makamai a ƙauyen Pakachi na Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin, Kyaftin Oya James ya fitar ranar Laraba, ya ce an samu wannan nasarar ce a ƙoƙarinta na wanzar da zaman lafiya da dakile masu aikata miyagun laifuka da ke tada zaune tsaye a yankunan Filato.

A cewar sanarwar, “dakarun rundunar Hakorin Damisa IV a wani samame, sun gano wani waje da aka mayar da shi na ƙera makamai a can wani tsauni a ƙauyen Pakachi na ƙaramar hukumar Mangu,”

Bindigogi da tarin makamai da aka gano
Sauran tarin makamai da aka gano

A yayin samamen, an gano makamai masu yawa tare da kama wani mutum ɗaya.

“An kama wani mutum mai suna Mista Tapshak Plangji mai shekara 25 da ake zargin yana da hannu a haramtattun ayyuka a masana’antar,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Ta kuma ce ainihin mamallakin masana’antar mai suna Mista Nuhu Meshack ya gudu amma ana neman sa don gurfanar da shi a gaban shari’a.

Makaman da rundunar ta gano a masana’antar sun haɗa da bindiga samfurin AK47 guda tara, da jigidar harsasai 16 da ƙananan bindigogi 11 da zarto uku da gudumomi da injin tono da sauran manyan makamai.

Mista Plangji da duka makaman da aka samu suna wajen rundunar sojin don yin bincike.

Rundunar ta kuma sha alwashin ci gaba da aiki ba kama hannun yaro don gano duk wasu ɓata gari masu mummunar aniya wajen tarwatsa zaman lafiya a jihar da ma fadin Nijeriya.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan samame na zuwa ne makonni kadan bayan kashe-kashe da rikicin da aka dinga samu a jihar ta Filato, wadanda suka jawo asarar dumbin rayuka da dukiyoyi.

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja

Zulum ya kaddamar da taron gyara karatun tsangaya a Borno