Sojoji sun gano masana’antar ƙera bindigogi a Kudancin Kaduna
Mun kama wani dillalin makamai da ke hada-hadar bindigogi a Kaduna da Filato.
Rundunar Sojojin ‘Operation Safe Haven’ ta gano wata masana’antar ƙera bindiga a Karamar Hukumar Jema’a da ke Jihar Kaduna.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, rundunar sojin ta samu nasarar cafke wani da ake zargi mai suna Napoleon John da ke yankin na Kudancin Kaduna da ya yi kaurin suna wajen rikice-rikice a shekarun baya.
- Jamus ta naɗa Julian Nagelsmann kociyan tawagar ƙasar
- Dalibai 35 ’yan ta’adda suka sace a Jami’ar Tarayya ta Gusau —Gwamnati
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Rundunar Sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X wanda a bayan ake kira Twitter a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce nasarar ta su ta biyo bayan binciken leken asiri da su ka dauki mako guda suna gudanarwa, inda sunan Napoleon John ya kasance cikin wadanda suke nema ruwa a jallo.
Wanda ake zargin ya tabbatar da kasancewar hannunsa dumu-dumu cikin badaƙalar ƙera bindigogi.
Napoleon ya jagoranci rundunar ta OPSH zuwa wani waje da sanarwar bata bayyana ba, inda suka gano inda ake ƙera makamai daban-daban tare da cafke wani mai safarar makaman mai suna Monday Dunia wanda shi ma ya tabbatar da hannunsa dumu-dumu cikin badakalar da yac e ya shafe fiye da shekara biyar yana hada-hadar bindiga a jihohin Kaduna da Filato.
“Biyo bayan zurfafa binciken da mu ka yi mun kai ga gano masana’antar da ake kera makamai tare da kama nau’o’in makaman da suka hada da AK 47 kirar gida da irin ta sojoji da karamar bindigar mashin gun da sauransu,” inji sanarwar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa tuni rundunar ta baza komarta domin kamo jagoran badakalar da ya arce, wanda ta sha alwashin za ta cika hannunta da shi nan da kankanin lokaci.