Sojoji sun gano ramukan da ’yan Boko Haram suka boye makamai

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da suke aiki a karkashin shirin Zaman Lafiya Dole tare da hadin gwiwar mayakan sa-kai na Sibiliyan JTF sun gano wasu ramuka da ’yan Boko Haram suka boye dimbin makamai a ranar Asabar da ta gabata a yankin Borgozo – Alargano.Wata sanarwa da Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman […]

Sojoji sun gano ramukan da ’yan Boko Haram suka boye makamai
Sojoji sun gano ramukan da ’yan Boko Haram suka boye makamai

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da suke aiki a karkashin shirin Zaman Lafiya Dole tare da hadin gwiwar mayakan sa-kai na Sibiliyan JTF sun gano wasu ramuka da ’yan Boko Haram suka boye dimbin makamai a ranar Asabar da ta gabata a yankin Borgozo – Alargano.
Wata sanarwa da Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar ta ce sojojin sun gano akwatuna kimanin 36 makare da bindigogi da harsasai bayan sojojin sun fatattaki mayakan Boko Haram a dajin yankin Alagarno da suka hada da Kadari da Camp Abu Fatima da Gursum. Kuma sojojin sun gano wata mota kirar Hilud guda daya da janareto daya da kuma Babura da dama.
Harsasan da mayakan Boko Haram din suka boye a karkashin kasa samfurin na kungiyar Tarayyar Turai ne (NATO), sannan sojojin sun kuma gano dimbin abinci da Boko Haram din ta boye a karkashin kasa.