Sojoji sun halaka ’yan bindiga a Kudancin Kaduna
Sojojin Najeriya sun harbe ’yan bindiga guda hudu har lahira tare da kwato makamai a Jihar Kaduna. Rundunar Tsaro ta ce sojojin sun aika ’yan bindigar lahira ne a kauyen Jeka da Rabi a kan titin Kaduna zuwa Abuja, inda suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu daga hannun ’yan bindigar. Daraktan Yada Labaran Rundunar […]
Sojojin Najeriya sun harbe ’yan bindiga guda hudu har lahira tare da kwato makamai a Jihar Kaduna.
Rundunar Tsaro ta ce sojojin sun aika ’yan bindigar lahira ne a kauyen Jeka da Rabi a kan titin Kaduna zuwa Abuja, inda suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu daga hannun ’yan bindigar.
Daraktan Yada Labaran Rundunar Manjo Janar John Enenche ya ce ’yan bindigar sun gamu da gamonsu ne bayan dakarun rundunar Operation Accord sun samu labarin motsinsu daga Kachia.
Ya ce an yi musayar wuta da ’yan bindigar, inda hudu daga cikinsu kwanansu ya kare, wasu kuma suka sha da kayr da raunin harbin bindida.
Enenche ya ce sojoji na kara samun karfi a yankin Kudancin Kaduna mai fama da kasha-kashen kabilanci da na ’yan bindiga.