Sojoji sun halaka ’yan ta’adda masu sanye da kayan ’yan sanda a Zamfara

Sojoji sun halaka gungun wasu ’yan ta’adda da ke sanye da kayan ’yan sanda a hanyarsu ta kai wa al’umma hari a Jihar Zamfara

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda masu sanye da kayan ’yan sanda a Zamfara

Sojoji sun halaka gungun wasu ’yan ta’adda da ke sanye da kakin ’yan sanda a Karamar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara.

’Yan ta’addan sun gamu da ƙarar kwana ne a lokacin da suke kan hanyarsu da kai wa wani yanki hari.

Kakakin Rundunar Soji ta Operation Fashin Yamma, Laftanar-Kanar Abubakar Abdullahi, ya ce ’yan ta’addan guda biyu da aka kashe sun gamu da ƙarar kwana ne bayan da suka fara buɗe wa sojojin wuta.

Ya bayyana cewa an ƙwato bindiga ƙirar PKT Machine Gun guda ɗaya da kuma AK-47 a hannun ɓata-garin da aika barzahu.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano