Sojoji sun hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Sani Rusu a Zamfara
Dakarun sun hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da raunata wasu.
Sojojin Operation Hadarin Daji sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Sani Rusu, yayin wani samame da suka kai a Jihar Zamfara.
Dakarun sun kuma lalata sansanonin ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai.
- Gobara ta yi ajalin ’yar sakataren gwamnatin Sakkwato da ’ya’yanta 3
- Tukunyar iskar gas ta jikkata mai juna biyu da ’ya’yanta 4 da ma’aurata
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, ya ce: “A ranar 4 ga watan Janairu, sojoji sun kai farmaki ƙauyen Bamamu, da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda suka yi arangama da ’yan ta’adda.
“A yayin fafatawar, an kashe ƙasurgumin shugaban ’yan ta’adda, Sani Rusu.
“Haka kuma, a wannan rana, sojoji sun yi kwanton-ɓauna a Kwanar Jollof da ke Ƙaramar Hukumar Shinkafi, inda suka kashe wasu ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai, ciki har da bindigogi da alburusai.”
Ya ƙara da cewa an gudanar da luguden wuta ta sama a ranakun 30 ga watan Disamba da 2 ga watan Janairu, inda aka kai farmaki kan sansanonin Bello Turji da Ibrahim Chumo.
“Waɗannan hare-haren sun janto wa ’yan ta’adda mummunar asara, inda da dama suka mutu ko suka ji rauni, kuma an lalata mafakarsu,” in ji Abdullahi.
Rundunar ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da haɗin kai, tare da tabbatar da ƙudurinta na kawo ƙarshen ta’addanci a yankin.