Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina
Dakarun sun gano maɓoyarsu tare da yi musu ruwan bama-bamai.

Dakarun Sojin Saman Najeriya (NAF), sun kashe manyan shugabannin ’yan bindiga guda biyu, Gero (Alhaji) da Alhaji Riga, tare da wasu mayaƙansu sama da 20 a wani hari ta sama da suka kai a Jihar Katsina.
Harin ya faru ne a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.
- Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Amurka kan cin zarafin Kiristoci
- Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin Kano
Rundunar Operation Fansan Yamma ta NAF ce ta ƙaddamar da harin bayan samun sahihan bayanai kan maɓoyar maharan.
A cewar Mataimakin Kakakin NAF, Kyaftin Kabiru Ali, ya ce dakarun sun lalata sansanin maharan.
“An kashe ƙarin ‘yan ta’adda a tsaunukan da ke kusa, kuma har yanzu ana ci gaba da binciken irin ɓarnar da aka yi musu,” in ji shi.
Gero da Riga sun shahara wajen bai wa ‘yan ta’adda mafaka, waɗanda ke yawan kai matafiya hare-hare a kan titin Funtua zuwa Gusau.
Mutuwarsu ta zama babban ci gaba ga jami’an tsaro da ke aiki tuƙuru don tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
“Wannan babban ci gaba ne a yaƙin da muke yi da ɓarayin daji a Katsina da kewaye.
“Sojojin sama tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasa za su ci gaba da kai wa maɓoyar ‘yan ta’adda hare-hare har sai an samu cikakken zaman lafiya,” in ji shi.