Sojoji sun hallaka ’yan bindiga 11 a Katsina da Zamfara
Dakarun sun kai samame daban-daban tare da hallaka maharan.
Dakarun Sojin Najeriya sun kai samame wasu maboyar ’yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara, inda suka yi nasarar kashe 11 daga cikinsu.
Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X (Twitter), a ranar Litinin.
- An Dakatar Da Shugabar APC A Kaduna Kan Caccakar Uba Sani
- Mutane Sun Fasa Rumbun Abincin Gwamnati A Jihar Kebbi
Rundunar ta ce a wani samame da suka kai a Zamfara a ranar 29 ga watan Maris, sun yi nasarar tarwatsa maboyar kasurgumin dan bindiga, Hassan Yantagwaye, a Karamar Hukumar Tsafe.
Sanarwar ta kara da cewa, Yantagwaye da yaransa ne ke da alhakin sace mutane da ayyukan ta’addanci a wasu yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.
“A yayin farmakin, sojoji sun fatattaki ’yan bindigar a wani artabu da suka yi, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da kwato muggan makamai da alburusai a maboyarsu.
“A Jihar Katsina kuwa, a ranar 30 ga watan Maris, sojoji sun yi artabu da ‘yan bindiga a yankunan Shawu Kuka, Shinda, Tafki, Gidan Surajo, da Citakushi a Kabai I da Kabai II duk a Karamar Hukumar Faskari.
“Sojojin sun kashe ’yan bindiga takwas tare da kwato bindigogi guda uku kirar gida, kakin soji da kuma kayan abinci,” in ji sanarwar.
Rundunar ta ce tana ci gaba da yaki da ’yan ta’adda domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihohin da ma Najeriya baki daya.