Sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 5, wasu 44 sun miƙa wuya a Borno

Dakarun sun ce hare-haren da suke kai wa ‘yan ta’addan ya sa wasu suka miƙa wuya.

Sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 5, wasu 44 sun miƙa wuya a Borno

Rundunar Sojin Najeriya, ta sanar da cewar dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da kama wasu 44 da suka miƙa wuya a Jihar Borno. 

Wannan na ɗauke cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X (twitter), a ranar Talata.

A yayin ayyukansu, sojojin sun gano abubuwa masu fashewa, makamai, alburusai, da shanun da aka sace, sannan sun kama wasu masu laifi.

Sojojin, sun bayyana cewa a ranar Litinin, sun kai hari sansanin ’yan ta’addan ISWAP da ke yankin Bama a Jihar Borno.

A wannan samame, sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da ƙwato wasu abubuwa kamar bam, RPG, bindigogi guda biyu, AK-47, alburusai 23, babura guda shida, da kuma wasu magunguna.

Kazalika, sojojin sun ce sakamakon ci gaba da kai hare-hare a yankin Arewa Maso Gabas, ’yan Boko Haram guda 44 da iyalansu sun miƙa wuya ga dakaru a yankunan Bama, Dikwa, da Gwoza na Jihar Borno.