Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 148, sun kama wasu 258

Rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin Najeriya.

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 148, sun kama wasu 258

Rundunar Sojin Najeriya, ta samu gagarumar nasarar kashe ‘yan ta’adda 148 tare da kama wasu 258 a hare-haren da suka kai.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaron ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa an kama mutum biyu da ake zargi da safarar harsasai.

Waɗanda ake zargin su ne Danweri da Abubakar Hamza.

Haka kuma, an samu nasarar gano ƙunshin harsasai biyu a Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a Jihar Bauchi.

Bincike ya gano an yi amfani da su wajen ayyukan ta’addanci.

Manjo Janar Buba ya yi wannan bayani ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Wannna zuwa ne bayan da rundunar ta ci gaba da zage damtse wajen yaƙi da ’yan ta’adda a faɗin Najeriya.