Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 2 a Zamfara
Sojojin sun hallaka maharan bayan wani artabu da suka yi.
Dakarun runduna ta 1 na rundunar Sojin Najeriya, sun kashe ’yan bindiga biyu yayin wani artabu a yankin Unguwar Sarkin Musulmi da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar Sulaiman Omale, ya fitar a Gusau a ranar Lahadi.
- Masu kamuwa da cutar ƙyandar biri na ƙaruwa a Afirka — AU
- Abba ya ba da umarnin bincikar kwangilar magunguna
Omale, ya ce rundunar haɗin gwiwa ta sashe na 1 a Arewa maso Yamma, na ci gaba da samun nasarori a yaƙi da ’yan bindiga a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.
A ranar 16 ga watan Agusta, 2024, sojojin, ƙarƙashin umarnin kwamandan runduna ta 1, sun kashe ’yan bindiga biyu, yayin wani artabu a yankin Unguwar Sarkin Musulmi da ke Kaura Namoda.
Bayan samun sahihan bayanai, sojojin sun kai wa ’yan bindigar samame.
Bayan ɗaukar lokaci ana musayar wuta, dakarun sun kashe ’yan bindiga biyu, yayin da sauran suka gudu da raunukan bindiga.
Bayan artabun, sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano babur guda ɗaya da ’yan bindigar ke amfani da shi.
Omale, ya ce yanzu yankin ya samu tsaro, yayin da sojoji ke ci gaba da sintiri don tabbatar da tsaron al’ummar yankin.
Ya ƙara da cewa wannan nasarar da suka samu na nuna irin jajircewar da rundunar Operation Hadarin Daji na yaƙi da ’yan bindiga da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara.