Sojoji sun hana shiga da fita a fadar Shugaban Kasar Nijar

Nijar mai makwabtaka da Najeriya, ta yi fama da juyin mulki har sau hudu, kamar takwarorinta na yankin Sahel.

Sojoji sun hana shiga da fita a fadar Shugaban Kasar Nijar

Dakarun Gwamnatin Jamhuriyar Nijar. (Hoto: France24).

Sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar Nijar sun tsare daukacin hanyoyin shiga fadar gwamnatin da ma birnin Yamai, lamarin da ya haifar da rudani.

Kawo yanzu dai ba a kai ga tantance musabbabin daukar matakin da sojojin suka yi, sai dai kuma al’amura na gudana yadda aka saba, sannan babu wani rahoto game da daukar matakan soji.

Duk da haka, wasu rahotanni sun nuna cewa wasu tsofaffin shugabannin kasar sun fara tattaunawa da sojojin domin ganin sun mayar da wukarsu cikin kube.

Daga samun mulkin kanta a shekarun 1960, kasar Nijar mai makwabtaka da Najeriya, ta yi fama da juyin mulki har sau hudu, kamar takwarorinta na yankin Sahel.

Idan ba a manta ba, a jajibirin ranar rantsar da shugaba mai ci, Mohammed Bazoum a shekarar 2021, an yi yunkurin juyin mulki a kasar.