Sojoji sun harbe wani mai facin taya a Kaduna
Wani mai facin taya mai suna Dauda Abdullahi da ke sana’ar faci a mahadarTitin Abuja a Rigasa Kaduna ya rasa ransa, bayan da wani soja ya harbe shi a ranarJuma’ar da ta gabata. Wani makwabcin marigayin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, yana zaune bayan magriba kusa da inda marigayin ke sana’a, sai […]

Wani mai facin taya mai suna Dauda Abdullahi da ke sana’ar faci a mahadarTitin Abuja a Rigasa Kaduna ya rasa ransa, bayan da wani soja ya harbe shi a ranarJuma’ar da ta gabata.
Wani makwabcin marigayin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, yana zaune bayan magriba kusa da inda marigayin ke sana’a, sai ya ji karar harbi da ya duba sai ya ga ashe wani soja ne ya harbi Dauda a kafa, jini yana ta zuba.
“Daga bisani sojan ya dawo tare da wani abokin aikinsa inda suka dauke shi zuwa Asibitin Sojoji na 44. Washegari kuma da misalin karfe 3:00 na rana sai labari ya zo mana cewa Dauda ya rasu. Kuma sojojin ne suka kai gawar marigayin gidansa da ke Saman Taro-Taro a Titin Lakwaja,” inji shi.
Ya ce ba su san abin da marigayin ya yi wa sojan ba, kuma a saninsu marigayin ba mai tashin hankali ba ne, kuma galibi marigayin ne se yi wa sojojin faci ko karin iskar taya a motocinsu, saboda sojojin a Bakin Ruwa suke.
Sai dai wani dan acaba da al’amarin ya faru a kan idonsa ya ce, wani soja sanye da kayan gida ne aka kwace masa wayar salularsa a Titin Abuja, hakan ya sa ya koma Bakin Ruwa ya kira abokan aikinsa. Ya ce da isowarsu sai wadanda suka kwace wayar suka fita da gudu, ganin haka sai daya daga cikin sojojin ya yi harbi, sai harsashi ya samu Dauda a kafa.
Marigayin wanda ya bar da daya mai kimanin shekara biyu da matarsa mai juna biyu, ta bukaci hukuma ta bi musu hakkinsu.
Kakakin Runduna ta daya ta Sojan Najeriya da ke Kaduna Kanar Usman Abdul ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce hakan ya faru ne bisa kuskure. Ya ce za su ba iyalan mamacin tallafi da kular da ta dace.