Sojoji sun harbi dan sandan da ya jagoranci ’yan Ombatse suka kai musu hari
Sojojin sun ce sun bindige akalla ’ya’yan kungiyar Ombatse 10 tare da kame da dama ciki har da wani dan sandan kwantar da tarzoma (Mopol) da ake zargin ya jagoranci kai musu hari a wurin duba ababen hawa a ranar Talatar da ta gabata. dan sandan da ake zargin mai suna Kofur Ekipi Mala an […]
Sojojin sun ce sun bindige akalla ’ya’yan kungiyar Ombatse 10 tare da kame da dama ciki har da wani dan sandan kwantar da tarzoma (Mopol) da ake zargin ya jagoranci kai musu hari a wurin duba ababen hawa a ranar Talatar da ta gabata.
dan sandan da ake zargin mai suna Kofur Ekipi Mala an ce yana aiki ne da Hedkwatar Mopol ta 45 da ke Abuja, kuma an iske katin shaidar aikinsa a tare da shi yana sanye da yunifom din aikisa.
Wani Laftana na soja da ya ki ambatar sunansa ya shaida wa manema labarai a gidan gwamnatin jihar cewa sun kashe ’yan Ombatsen ne a wurin duba motoci na sojoji da ke mahadar Alushi a hanyar Akwanga zuwa Keffi, inda wadanda ake zargin ’yan kungiyar matsafan kusan 200 suka kai hari ga sojojin su kuma suka mayar da martani.
Ana zargin dan sandan da samar da makamai ga mayakan kungiyar Ombatse, kuma an iske shi da guraye da dagage a jikinsa.
Mafi karancin shekaru daga cikin’yan Ombatsen da suka kai harin, wanda shi ma aka kai shi gidan gwamnati tare da dan sandan da sauran wadanda aka kama a wata Toyota Hilud ya tabbatar da cewa dan sandan da ake magana, shi ne yake samar musu da bindigogin da suke aikata ta’asa da su.
Wasu daga cikin hotunansu da aka baje sun nuna matasansu rike da bindigogi kirar AK 47, wadanda aka ce wani dan sandan ne ya kawo musu daga Abuja.
Gwamna Al-Makura wanda ya ce ya kadu kan lamarin, ya ce zai yi wa jama’ar jihar jawabi ta kafafen watsa labarai, bayan ya samu bayani daga jami’an tsaron jihar.
Kakakin ’Yan sandan Nasarawa Cornelius Ocholi, wanda ya tabbatar da lamarin ta tarho ya ce an kashe wasu mahara uku a yayin rikicin kuma an kai hudu daga cikinsu da suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na dahaltu Araf da ke Lafiya don yi musu jinya.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce ’yan kungiyar Ombatse suka sake kai hari a garuruwan Obi da Assakiyo, inda suka rika kashe mutane suna kone gidaje.
Wani mazauna Obi da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu ’yan kabilar Alago suka tare wata bas a hanyar Obi zuwa Keana dauke da wasu mutane don su bincika ko su wane ne. Ya ce da suka gano ’yan kabilar Eggon ne sai suka tambaye su inda za su je. Ya ce mutanen Eggon din sun ce wucewa kawai za su yi. To amma kasancewar ana zaman doya da manja a tsakanin kabilun biyu sai mutanen Alago suka ki amincewa da haka.
Majiyar ta ce ana cikin haka ne sai fada ya barke tsakaninsu inda aka raunana wani daga cikin mutanen Eggon, sai ’yan uwansa suka koma suka taho da ’yan kungiyar Ombatse suka shiga garin da makamai suna kashe mutane da kone gidaje.
Majiyar ta ce sun shiga garin Assakio a kusa da Obi inda kabilar Alago ta fi yawa suka ci gaba da kashe-kashe da kone-konen gidajen jama’a, lamarin da ya tilasta mazauna garuruwan musamman mata da yara suka gudu zuwa makwabta kamar Keana da Awe da Agyaragu da Lafiya galibi a kafa.