Sojoji sun kama durum din fetur 4000 da za a kai wa Boko Haram
Rundunar Sojojin Saman Nijeriya ta bayyana cewa ta dakile wani yunkuri na kai wa mayakan Boko Haram man fetur bayan da ta tare hanyar da ake kai musu kayayyaki a iyakar Najeriya da Kamaru. Daraktan Labarai na Rundunar Sojojin Saman Iya Kwamando Dele Alonge ya ce rundunar ta kama wasu durarrukan man fetur dubu hudu […]
Rundunar Sojojin Saman Nijeriya ta bayyana cewa ta dakile wani yunkuri na kai wa mayakan Boko Haram man fetur bayan da ta tare hanyar da ake kai musu kayayyaki a iyakar Najeriya da Kamaru.
Daraktan Labarai na Rundunar Sojojin Saman Iya Kwamando Dele Alonge ya ce rundunar ta kama wasu durarrukan man fetur dubu hudu da wasu jarkoki shake da mai da sauran wasu kayayyaki da aka yi safararsu don kai wa Boko Haram a daidai kauyukan Pepe da Dashin-Hausa da Belel Bilachi da Konkul da suke iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Kamaru a ranar Talata.
Sojojin sun yi nasarar kama kayayyakin sakamakon sintirin da suke yi a jirgin sama, inda suka gano ana jigilar su ta cikin ruwa.
Rundunar ta kara da cewa tana kan gano sansanin ’yan Boko Haram tare da tarwatsa su a yayin sintirin da take gudanarwa.