Sojoji sun kama haunin Boko Haram a Bauchi

’Yan sanda sun ce sun kama babban kwamandan ’yan Boko Haram da aka fi sani da “Babban Hauni” a wani farmaki da suka kan a sansanin ’yan Boko Haram a Jihar Bauchi. Haunin mai suna Muhammad Zakari, mai shekara 30, an kama shi ne ranar Asabar sakamakon “gagarumin harin da jami’an tsaro suka kai kan […]

Sojoji sun kama haunin Boko Haram a Bauchi
Sojoji sun kama haunin Boko Haram a Bauchi

’Yan sanda sun ce sun kama babban kwamandan ’yan Boko Haram da aka fi sani da “Babban Hauni” a wani farmaki da suka kan a sansanin ’yan Boko Haram a Jihar Bauchi. Haunin mai suna Muhammad Zakari, mai shekara 30, an kama shi ne ranar Asabar sakamakon “gagarumin harin da jami’an tsaro suka kai kan sansanin ’yan kungiyar da ke dajin Balma a Jihar Bauchi kamar yadda wata sanarwar ’yan sanda ta ce.
Ana zargin Zakari da hannu a “yanka mutum bakwai ciki har da mata da yara na kwanan nan.” Kuma a cewar ’yan sandan dajin na Balma yah ade da dazukan Arewa maso Gabas da mayakan kungiyar ke amfani da shi kuma suka kashe sama da mutum dubu 10 a hare-haren da suka kaddamar shekara biyar da suka gabata.
Zakari dai ba wani sanannen malami ba ne, amma tsarin shugabancin kungiyar ba a tsare yake ba inda yake da rukunoni masu zaman kansu da daidaikun shugabannin ke gudanarwa ba tare da kai rahoto ga wani fitaccen shugaba ba.