Sojoji sun kama mai samar wa Boko Haram mai da abinci
Sojojin da ke fafatawa da mayakan Boko Haram sun samu nasarar kama wani mutum da ake zaton shi ne yake samar wa ’yan Boko Haram din da man fetur da kayan abinci, a kauyen Daban Shata da ke garin Baga a karamar Hukumar Kukawa a Jihar Borno. Sojojin sun kama shi ne a bayan sanya […]
Sojojin da ke fafatawa da mayakan Boko Haram sun samu nasarar kama wani mutum da ake zaton shi ne yake samar wa ’yan Boko Haram din da man fetur da kayan abinci, a kauyen Daban Shata da ke garin Baga a karamar Hukumar Kukawa a Jihar Borno.
Sojojin sun kama shi ne a bayan sanya ido da bi sawunsa inda suka gano yana kai wa ’yan ta’addan kayan masarufi a ranar Lahadin da ta gabata.
A ’yan kwanakin nan Rundunar Sojin Najeriya tana bayyana samun nasara a kan kungiyar Boko Haramu a samamen da take kaiwa dajin Sambisa inda nan ne sansanin Boko Haram, mafi girma inda suka ce sun kubutar da akalla mata da yara kusan 700, a cikin mako daya.
kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya, wato Amnesty International, ta ’yan Boko Haram sun sace mata fiye da 2000 a bara kawai baya ga ’yan matan Chibok da suka sace daga makaranta, wadanda har yanzu ba a gano ko daya daga cikinsu ba a tsakanin matan da aka kubutar.