Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane a Yobe

Sojojin sun ƙwato bindigogi nau’in AK-47 guda uku ƙira gida da bindigar pistol guda ɗaya ƙirar gida, harasashi iri-iri da kuma wayoyin hannu guda huɗu da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan laifuka na waɗanda aka kama.

Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane a Yobe

Sojojin Sashe na 2 (Sector 2) na Rundunar Operation HADIN KAI, tare da haɗin gwiwar Kungiyar Maharba ta Jihar Yobe, sun kama mutane biyar da ake zargi da garkuwa da mutane yayin wani samame na sirri a ƙauyen Jegalari da ke Karamar Hukumar Fune a Jihar Yobe.

Samamen, wanda sojojin Bataliya ta 233 da ke aiki a sansanin sojoji na Damaturu suka gudanar a ranar 23 ga Yuli, 2026, ya biyo bayan bayanai na sirri ingantattu game da ayyukan mutanen da ake zargi da aikata laifuka a yankin.

Sojojin sun ƙwato bindigogi nau’in AK-47 guda uku ƙira gida da bindigar pistol guda ɗaya ƙirar gida, harasashi iri-iri da kuma wayoyin hannu guda huɗu da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan laifuka na waɗanda aka kama.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Mai Magana da Yawun Rundunar Sojoji na wucin gadi na Hedikwatar Haɗin Gwiwa ta (Arewa ta Gabas ) Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce waɗanda ake zargin suna tsare a hannun sojoji domin ci gaba da bincike.

“A halin yanzu waɗanda ake zargin suna hannun sojoji tare da kayayyakin da aka ƙwato domin ci gaba da bincike don tabbatar da sa hannunsu a aikin garkuwa da mutane da sauran laifuka masu alaƙa,” in ji Goni.

Rundunar sojin ta ce, samamen na ɗaya daga cikin ƙoƙarin da ake yi na hana ƙungiyoyin masu laifuka sakewa ko gudanar da ayyukansu a fadin Arewa maso Gabas.

“Rundunar Operation HADIN KAI ta kasance tsayayya wajen sadaukar da kanta don hana ’yan ta’adda da sauran masu laifuka damar yin abin da suka ga dama a faɗin Arewa maso Gabas ta hanyar ci gaba da gudanar da samame na sirri,” in ji sanarwar.

Haka zalika, sojojin sun ƙarfafa wa mazauna yankin gwiwa da su kasance masu sa ido da kuma taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan sirri da za su taimaka wajen hana ayyukan laifuka.

Obasanjo na yunƙurin ɓata min suna don ɗan takararsa — Atiku

Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane a Yobe

Na yi wa majinyata 15 magani — Likitan bogi

Rikicin fili: Gwamnatin Jigawa ta raba gonaki ga manoman iyakar ƙasa