Sojoji sun kama masu kitsa kashe-kashe a Jihar Taraba
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da suke gudanar da shirin tabbatar da zaman lafiya mai taken Edercise Ayem Akpatuma, a ranar Juma’ar da ta gabata, sun kama mutum biyu masu suna Mista dan’asebe Gasama da Mista danjuma da ake kira da American kan zarginsu da kitsa kashe-kashe da tayar da hankali a kananan hukumomin […]

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da suke gudanar da shirin tabbatar da zaman lafiya mai taken Edercise Ayem Akpatuma, a ranar Juma’ar da ta gabata, sun kama mutum biyu masu suna Mista dan’asebe Gasama da Mista danjuma da ake kira da American kan zarginsu da kitsa kashe-kashe da tayar da hankali a kananan hukumomin Takum da Ussa da ke Jihar Taraba.
Kakakin Rundunar Bigediya Janar Tedas Chukwu, ya fadi a wata sanarwa a ranar Asabar cewa wadanda ake zargin an kama su ne a garin Takum “sakamakon samun bayanan sirri da suka tabbatar cewa su ne suke tsara hare-haren da ake kaiwa ga Fulani da kabilun yankin.”
Sanarwar ta ce: “Binciken farko ya kara gano cewa wadannan mutum biyu su ne manyan masu taka rawa wajen kashe-kashen da tayar da zaune-tsaye a kananan hukumomin biyu da ke jihar. Kuma ana bukatar jama’a su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wa hukumomin tsaro wajen daukar matakan da suka dace a kan lokaci.”
Birgediya Janar Chukwu ya kuma musanta zargin da ake yi cewa Rundunar Sojin Najeriya tana nuna son kai da karkata ga dangi wajen daukar sojoji a aiki.
Ya ce, “Wasu labarai da suke karakaina a kafofin sadarwar zamani suna zargin Rundunar Sojin da tauye wadansu da kuma hana wasu kabilu ’yancin shiga aikin soja a daukar sojoji da ake yi yanzu sun jawo hankalin rundunar.”
Kuma “Rundunar Sojin Najeriya tana fadi da babbar murya cewa wannan zargi zuki ta malle ce, kuma kazafi ne babu kanshin gaskiya a cikinsa. Kuma aiki ne na marasa kishin kasa da suke son bata sunan Rundunar Sojin Najeriya. Domin kawar da duk wata shakka da fito da hakikani gaskiya, Rundunar Sojin Najeriya tana sanar da cewa duk wani dan Najeriya ya cancanci a dauke shi a aikin soja, matukar ya cika sharuddan da aka gindaya na daukarsa a sojan kuma Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da kauce wa tsoma kanta a harkokin siyasa wajen gudanar da ayyukanta da tsarin mulki ya ba ta kuma ta taimaka wa gwamnatin farar hula,” inji sanarwar.
Ta kara da cewa: “Babu wata jiha a kasar nan ciki har da Jihar Adamawa da za a dakile kamar yadda masu mugun nufi suke zargi. Dukan masu neman shiga soja daga kananan hukumomin Demsa da Numan da Lamurde da kuma Girei yanzu haka ana damawa da su a harkar daukar soji kamar kowane mai nema. Rundunar Sojin Najeriya tana shawartar dukan masu fatan alheri ga kasar nan su yi watsi da wancan zargi marar tushe da kirkirra marubucinsa ne kawai.”
Janar Chukwu ya kara da cewa: “Zargin cewa Rundunar Sojin ta zabi wata kabila daga Kudu maso Gabas tsagwaron karya ce. Yana da kyau a fahimci cewa Rundunar Sojin Najeriya ba ta goya wa wata kabila ko wani addini baya.”