Sojoji sun kama mataimakin shugaban karamar hukumar Anka

Rundunar sojojin Najeriya na “Operation Sharan Daji”  a jihar Zamfara sun kama mataimakin shugaban karamar hukumar Anka Yahuza Wuya akan zarginsa da alaka da ‘yan bindigar da suka addabi jama’ar jihar. Mukaddashin jami’in yada labarai na rundunar sojojin Manjo Clement Abiade, ne tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Alhamis a Abuja. Manjo Clement, […]

Sojoji sun kama mataimakin shugaban karamar hukumar Anka

Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya na “Operation Sharan Daji”  a jihar Zamfara sun kama mataimakin shugaban karamar hukumar Anka Yahuza Wuya akan zarginsa da alaka da ‘yan bindigar da suka addabi jama’ar jihar.

Mukaddashin jami’in yada labarai na rundunar sojojin Manjo Clement Abiade, ne tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Alhamis a Abuja.

Manjo Clement, ya ce jami’an sun kama Yahuza Wuya ne tun ranar 13 ga Afrilu 2019 don yi masa bincike game da alakarsa da ‘yan bindiga a unguwar Sunke.