Sojoji sun kama mutum uku da ake zargi da satar shanu

Majiyoyin tsaro sun ce, aikin ya biyo bayan bayanan sirri da wani mazaunin yankin, Malam Muhammadu Ardo ya bayar game da zargin satar shanu a yankin.

Sojoji sun kama mutum uku da ake zargi da satar shanu

Sojojin Bataliya ta 212 da aka tura zuwa sansanin Forward Operating Base (FOB) Tuba sun kama wasu mutane uku da ake zargi da satar shanu a wani samame da suka kai a yankin Karnuwa cikin jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce, aikin ya biyo bayan bayanan sirri da wani mazaunin yankin, Malam Muhammadu Ardo ya bayar game da zargin satar shanu a yankin.

An ruwaito cewa, sojojin sun taru zuwa Karnuwa da misalin qarfe 12:30 na rana tun a ranar 4 ga Mayu, 2026, inda suka kama waxanda ake zargin da sunan Malam Mohammad Abatcha, mai shekara 28; Malam Mamman Bukar, mai shekara 18; da Malam Modu Hassan, mai shekara 30.

A cewar majiyar, an kama waxanda ake zargin ne yayin da suke amfani da motar xaukar kaya mai lambar rajista WW 806 GZ Delta, wacce ake zargin an xauke ta ne wajen jigilar shanun da aka sace.

Majiyar tsaron na cewa, an gano shanun da aka sace kuma nan take aka miqa su ga masu wurin da aka kama su.

Abubuwan da aka samu daga hannun waxanda ake zargin sun haxa da: baka da kibiya, wayoyin hannu guda uku, katunan shaidar xan qasa guda biyar da kuma kuxi Naira 20,650.

Binciken farko ya nuna cewa, waxanda ake zargin sun amsa laifin satar shanu da ake yawaita sata a Maiduguri akai-akai.

Majiyoyin tsaron sun qara bayyana cewa, masu bincike suna zargin akwai alaqa tsakanin waxanda ake zargin da kuma mambobin qungiyar ’yan ta’addan ISWAP da kuma Boko Haram saboda zargin rashin daidaito da aka lura a cikin bayanansu yayin amsa tambayoyin da ake musu.