Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Nabamamu a Zamfara

Ana sa ran cafke shi zai rage tasirin hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Nabamamu a Zamfara

Dakarun Sojin ‘Operation FANSAN YANMA’, sun kama Ƙasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu, wanda ya addabi al’ummar Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara.

Dakarun sun kai farmaki Hegin Mahe, Ruwan Bore, garin Mada, a Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Bayan musayar wuta, sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga, yayin da Nabamamu ya tsere zuwa cikin wani gida, amma daga ƙarshe dakarun suka cafke shi.

Bayan kama shi, ɗaya daga cikin yaransa, Bakin Malam, ya jagoranci kai harin ramuwar gayya wasu ƙauyuka, wanda ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa.

Sai dai dakarun sun mayar da martani, inda suka fatattaki ’yan bindigar, tare da ƙara jibge sojoji don tabbatar da tsaro a yankin.

Nabamamu, ya kasance almajiri ne, daga baya ya zama hatsabibin ɗan bindiga wanda ya yi sanadin ajalin mutane masu yawan gaske.

Ya jagoranci sama da mayaƙa 100, inda yake karɓar haraji daga hannun mazauna wasu ƙauyuka, kuma yana da alaƙa da masu yi wa wasu mahara safarar makamai a yankin.

Kama shi na iya rage ƙarfin ’yan bindiga a Zamfara, yayin da sojoji ke ƙara ƙaimi domin kawar da barazanar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn

Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano

An ga watan Ramadan a Najeriya

Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki