Sojoji sun kama wanda ya ‘kashe’ Janar Shuwa
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama wani da take zargin ya kashe Manjo-Janar Muhammad Shuwa mai ritaya. Kakakin rundunar sojin, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook jiya Litinin, inda ya ce: “Jami’an sojin dake tattara bayanan sirri sun kama wadanda ake zargi da kisan Manjo-Janar Mohammed Shuwa, […]

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama wani da take zargin ya kashe Manjo-Janar Muhammad Shuwa mai ritaya.
Kakakin rundunar sojin, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook jiya Litinin, inda ya ce: “Jami’an sojin dake tattara bayanan sirri sun kama wadanda ake zargi da kisan Manjo-Janar Mohammed Shuwa, mai ritaya.”
Kwamandan rundunar ta uku ta sojin Najeriya ya gabatar da shi a gaban manema labarai a Jihar Kano.