Sojoji sun kama ’yan aiken ’yan bindiga a kasuwar Kaduna
Ana zargin direban da masu sana’ar gawayin da yi wa ’yan bibdiga cefanen kayan da suke bukata a kasuwanni
Sojoji sun damke wani direban a-kori-kura da dillalan gawayi guda biyu kan zama ’yan aike ga ’yan bindiga a kananan hukumomin Kagarko da Kachia na jihar Kaduna.
Wani shugaban al’umma a daya daga cikin yankunan da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce so ji sojoji sun kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis a babbar kasuwar Kagarko bayan samun bayanan sirri kan su.
Ya ce wadanda ake zargin suna sayen miyagun kwayoyi da kayan abinci da lemon kwalba su kai wa ’yan fashin dajin.
- ’Yan bindiga sun kashe mutane 4 sun sace 150 a Zamfara
- Yadda mutumin da ya kashe mata 42 ya shiga hannu
Ya ce, “A baya sojojin sun samu bayanan sirri kan yadda direban da dillalan gawayin biyu suka saba siyan kayan abinci da magunguna ga ’yan fashin dajin domin a ba su damar yin gawayi a dajin.”
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ya zuwa yanzu bai tabbatar da kamen ba.