’Yan bindiga sun shiga hannu wurin ba wa sojoji cin hanci a Taraba
Masu garkuwa da mutane da ake neman su ruwa a jallo sun yi wa sojoji tayin cin hancin miliyoyin Naira, amma sojoji suka damke su
Rundunar Sojin Najeriya a jihar Taraba ta ce dakarunta sun kame wasu ’yan bindiga da suka yi musu tayin cin hancin Naira miliyan biyu.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na Rundunar ta Shida da ke Jalingo, Laftanar Oni Olubodunde ne ya sanar da kama wadanda ake zargin a kauyukan Chinkai da kuma Sarkin Kuduu da ke kananan hukumomin Wukari da Ibbi da ke jihar.
Ya ce, sojojin sun yi nasarar cafke wasu ’yan ta’adda da suka nemi bayar da cin hancin Naira miliyan biyu domin a sake su.
Ya ce, sojojin sun ki amincewa su karbi cin hancin daga matasan hudu masu shekaru 2o zuwa 28.
Laftanar Oni, ya ce wadanda ake zargin suna cikin jerin wadan da aka jima ana nema ruwa a jallo saboda hannu kan garkuwa da mutane a Wukari da kewaye.
Babban Birget na 6, Birgediya Kingsley Chidebere Uwa, ya yaba wa sojojin saboda jajircewarsu da wajen bin doka da oda.
Ya ce, jajircewarsu ce ta kai ga nasarar da suka samu.