Sojoji sun kama ’Yan Yahoo 150 a kusa da bariki a Delta

A kusa da barikin sojoji aka bude makarantar koyon damfara ta intanet, inda sojoji suka kama matasa 150 a rana guda.

Sojoji sun kama ’Yan Yahoo 150 a kusa da bariki a Delta

Shagon na’uror8in kwamfuta ana duba intanet

Sojoji sun kama matasa kimanin 150 da ake zargi da damfara ta intanet a wata makarantar da ta shahara wajen horas da masu harkar da ke kusa da barikin sojoji.

Matasan da ake zargin sun shiga hannu sojojin Bataliya ta 3 ta sojin Najeriya ne a rukunin gidajen Army Estate da ke da ke makwabtaka da barikin sojoji a yankin Effurun da ke Karamar Hukumar Uvwie a Jihar Delta.

Majiya mai tushe ta ce Army Estate da ke rukunin gidajen manyan sojoji da fararen hula da suka yi ritaya ne, kuma ya yi kaurin suna da ayyukan zamba ta intanet.

Majiyoyin da suka nemi a boye sunayensu sun bayyana cewa “an kama kusan 150 daga cikinsu” a samamen da sojoji suka kai da sanyin safiyar Asabar.

“An tsare mutane kusan 90 da sanyin safiyar, daga bisa ni kuma aka kama karin wasu 50 daga cikin daren,” A cewar majiyar.

An yi kamen ne bayan rahotannin sirri kan Makarantar HK (Hustle Kingdom) wacce ta shahara wajen horar da masu son koyon amfani da intanet domin yin damfara.

Wani mai binciken ya kuma ce, an kama wanda ake zargi da mallakar Makarantar HK tare da abokanansa a yayin samamen.

“Sojojin sun mika wadanda ake zargin ga ’yan sanda da ke Ekpan a Uvwie, domin gurfanar da su gaban kuliya,” in ji shi.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Bright Edafe domin jin ta bakinsa, ya tabbatar da kamen amma bai yi karin bayani ba.

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos

Bakanuwa ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’yan sanda

Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin dubin watan Rajab