“Sojoji sun kasa kawo ƙarshen Turji kamar yadda Jonathan ya yi wa Boko Haram”

Sanatan ya ce akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki matasa aikin soji domin yi wa ƙasarsu hidima.

“Sojoji sun kasa kawo ƙarshen Turji kamar yadda Jonathan ya yi wa Boko Haram”

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu

Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya samu nasarar yaƙar Boko Haram a ƙarshen mulkinsa ta hanyar amfani da dakarun tsaro masu zaman kansu (PMC).

Ndume, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, yayin taron sake duba kundin tsarin mulkin 1999.

Ya bayyana yadda sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar PMC daga Afirka ta Kudu suka yi nasarar fatattakar Boko Haram daga Maiduguri a shekarar 2014.

Ndume, ya bayyana cewa, “Muna da manyan matsaloli guda uku a ƙasar nan: Boko Haram, ‘yan fashin daji, da kuma IPOB.

“Idan gwamnati ta mayar da hankali sosai kan waɗannan matsalolin, za a iya magance su cikin watanni shida zuwa shekara ɗaya.”

Ya ƙara da cewa, ’yan fashin daji ba su da horo sosai ko kayan aiki, kuma mafi yawan makaman da suke amfani da su na sojojin Najeriya ne da suka ƙwace.

Ya bayar da shawarar a yi amfani da fasahar zamani wajen gano maɓoyarsu.

Ya kuma yaba wa Shugaban Hafsan Sojin Najeriya da ya bayyana yadda rundunar ke fama da rashin kayan aiki.

Ya ce ya kamata a ɗauki ƙarin mutane aikin sojin Najeriya saboda matasa da yawa suna da sha’awar yi wa ƙasa hidima amma ba su da damarmaki.

Kazalika, Ndume ya bayyana yadda Boko Haram ta kai kololuwarta a shekarar 2014, amma a cewarsa Jonathan ya samu shawarar amfani da PMC daga Afirka ta Kudu, waɗanda suka yi aiki tare da sojojin Najeriya da matasa na gida don yaƙar Boko Haram daga Maiduguri.

Ya ce wannan mataki ya taimaka wajen rage wa Boko Haram tasiri a wurare kamar Tafkin Chadi, tsaunukan Mandara, da dajin Sambisa.

Ya yi imanin cewa, idan aka samu isassun sojoji da kayan aiki na zamani kamar jirgi mara matuƙi, za a iya kawo ƙarshen Boko Haram baki ɗaya.

Ndume, ya soki gwamnati kan rashin amfani da isassun kayan aiki da fasahar zamani wajen yaƙar ’yan fashin daji da ‘yan ta’adda, inda ya ce sojojin Najeriya ba su da isassun makamai na zamani da ake buƙata don yin yaƙi cikin inganci.

Ya yi kira ga gwamnati da ta mayar da hankali kan tsaro da jin daɗin ‘yan ƙasa, wanda ya ce akwai yunwa sosai a ƙasar nan, kuma yawancin gonakin da ake da su ba a iya noma su.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka