Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji
Majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Makama cewa Bello Turji da mayaƙansa sun tafka asara da ta wuce misali.
Rahotanni na cewa dakarun Rundunar Sojin Ƙasa na Nijeriya sun kashe ɗaya daga cikin ’ya’yan ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji tare da lalata rumbun abincinsa.
Ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa ranar Asabar a shafin X.
- Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza
- Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza
Makama ya ce sojojin da ke ƙarƙashin rundunar Fansar Yamma sun kai hari ta sama da ƙasa inda suka tarwatsa maɓoyar da ta tsugunar da Turji tare da mayaƙansa a yankin Fakai da ke Ƙaramar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara.
Daga cikin sansanan ’yan ta’addan da sojojin suka tarwatsa sun haɗa da Zangon Dan Gwandi, Zangon Tsaika, Zangon Kagara da kuma wata makaranta da Turji ya mayar rumbun adana kayan abinci da makamai.
Majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Makama cewa Bello Turji da mayaƙansa sun tafka asara da ta wuce misali.
“Mun kashe ɗansa da mayaƙansa da dama a yayin harin kuma a wannan lokaci mun jiyo muryar Turji yana neman wasu jagororin ’yan bindiga bakwai da su kawo masa agaji amma babu wanda ya amsa kiran a cikinsu,” inji majiyar.
A bayan nan ne Rundunar Sojin Nijeriya ta ayyana Turji a matsayin mutumin da sauran ƙiris ƙarar kwana ta cimma domin jaddada ɗamarar da ta yi na ganin bayansa nan ba da jimawa ba.
Bello Turji wanda ɗaya ne daga cikin sahun ’yan ta’addan da mahukunta suka ayyana nema ruwa a jallo, ya addabi wasu yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya musamman Zamfara da Sakkwato da kuma wasu jihohin Nijar da suka yi iyaka da Nijeriya.