Sojoji sun kashe yaran Gana uku a Benuwe
Rundunar sojojin Najeriya wanda a shirin su na ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun sanar da cewa, rundunar ta kashe mutum uku daga cikin yaran wadanda ake zargin shugaban masu tada zaune tsaye a yankin, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana a unguwar Zaki Biyam, a karamar Hukumar Ukum dake jihar Benuwe. Kwamandan rundunar […]
Rundunar sojojin Najeriya wanda a shirin su na ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun sanar da cewa, rundunar ta kashe mutum uku daga cikin yaran wadanda ake zargin shugaban masu tada zaune tsaye a yankin, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana a unguwar Zaki Biyam, a karamar Hukumar Ukum dake jihar Benuwe.
Kwamandan rundunar Manjo Janar Adeyemi Yekini, ne bayyana hakan yau Litinin a Makurdi babban birnin jihar lokacin da yake ganawa da manema labarai.