Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno
Bayan tafka artabu, sojojin sun gano gawar ’yan ta’adda uku, ciki har da babban kwamandansu, Amirul Fiya.
Dakarun Sojin Najeriya a Dajin Sambisa
Dakarun Sojin Bataliya ta 3 da ke sansanin FOB Rann, a Ƙaramar Hukumar Kala-Balge a Jihar Borno, sun daƙile wani hari da ISWAP suka kai.
Bayan tafka artabu, sojojin sun gano gawar ’yan ta’adda uku, ciki har da babban kwamandansu, Amirul Fiya.
- Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13
- Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki
Sojojin sun bayyana cewa wannan nasara ta zama naƙaso ga shugabancin ISWAP a yankin.
Rundunar, ta ƙara jadadda ƙudirinta na kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Gabas.
Sojoji da sauran haɗin gwiwar jami’an tsaro na ci gaba da fatattakar ’yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas.