Sojoji sun kashe barayin shanu 20 da kwato makamai a Zamfara

Rundunar sojojin Najeriya da ke kaddamar salon yaki na Operation Sharan Daji a jihar Zamfara sun kashe barayin shanu 20 tare da kwato bindigogi 24 da wasu makamai. Mukaddashin Daraktan watsa labarai Birgediya Janar John Agim ne ya sanar da hakan. A lokacin da yake gana wa da manema labarai akan nasarar da rundunar ta […]

Sojoji sun kashe barayin shanu 20 da kwato makamai a Zamfara

Rundunar sojojin Najeriya da ke kaddamar salon yaki na Operation Sharan Daji a jihar Zamfara sun kashe barayin shanu 20 tare da kwato bindigogi 24 da wasu makamai. Mukaddashin Daraktan watsa labarai Birgediya Janar John Agim ne ya sanar da hakan.

A lokacin da yake gana wa da manema labarai akan nasarar da rundunar ta samu da sauran hukumomin tsaro. Agim ya ce, a lokacin da rundunar ta kai samame ta kwato shanu dubu 1,444 da awakai 478 da rakuma 11  da jakuna 14 da raguna 56 da kuma akuyoyi 293.